News
Majalisar Dokokin Kano Ta Bada Umarnin Binciken Kuɗaɗen Tsaro Na Ƙananan Hukumomi 44 Cikin Mako Biyu

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta umarci Kwamitinta kan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu da ya gudanar da bincike kan yadda ƙananan hukumomi 44 na jihar suka yi amfani da kuɗaɗen tsaro da ake ware musu, tare da gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.
Matakin ya biyo bayan amincewa da wani ƙudiri da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Ghari/Tsanyawa, Garba Yau’u Gwarmai, ya gabatar a zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranta.
Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11
Yayin gabatar da ƙudirin, Gwarmai ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙauyen Yan Kamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa, inda ya ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari tare da kashe mutane da dama.
A cewarsa, maharan sun shigo yankin ne daga maƙwabciyar Jihar Katsina kimanin makonni uku zuwa huɗu da suka gabata, inda suka hallaka sama da mutum takwas, ciki har da wata mata mai juna biyu da ‘ya’yanta biyu. Ya ƙara da cewa wasu manoma biyar ma sun rasa rayukansu a harin.
Ya gargaɗi cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar tsaro na iya bazuwa zuwa wasu sassan jihar.
Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro da ke aiki a yankin na kula da iyakar Kano da Katsina ne, don haka akwai buƙatar a ƙara musu kayan aiki da sauran tallafin da zai ba su damar yaƙi da masu aikata laifuka yadda ya kamata.
Gwarmai ya ce hare-haren sun tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu saboda fargabar sake kai musu farmaki, lamarin da ya ce na barazana ga rayuwar al’umma da kuma samar da abinci.
Haka kuma ya buƙaci gwamnatin jihar ta samar wa jami’an tsaro ingantattun kayan aiki da matsugunai domin ƙarfafa ayyukansu.
Da yake mara wa ƙudirin baya, Mataimakin Kakakin Majalisar, Muhammad Bello Butu Butu, ya buƙaci al’ummomin Kano ta Arewa su ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro ta hanyar ba su sahihan bayanan sirri domin shawo kan matsalar.
Sauran mambobin majalisar da suka yi magana kan ƙudirin, ciki har da Jagoran ‘Yan Adawa, Usman Tasi’u Kiru, Salisu Ibrahim (Doguwa) da Inusa Haruna (Gwarzo), sun nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro tare da goyon bayan a gudanar da cikakken bincike kan yadda ake kashe kuɗaɗen tsaro.
Bayan kammala muhawara, majalisar ta amince da umurtar Kwamitinta kan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu ya binciki yadda aka kashe kuɗaɗen tsaro a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, tare da gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.
