Connect with us

News

Yadda Hayaƙin Janareta Ya Hallaka Saurayi Da Budurwa A Kuros Riba

Published

on

FB IMG 1783205917197

Wasu masoya biyu sun rasa rayukansu sakamakon shaƙar hayaƙin janareta a Ƙaramar Hukumar Kalaba ta Kudu, da ke Jihar Kuros Riba.

Rahotanni sun nuna cewa mamatan, Favour Uduak Smith da saurayinta, Akpan, sun koma wani sabon gidan haya ne kwanaki kaɗan kafin faruwar lamarin.

Sarkin Karaye: Mun Daɗe Muna Wayar Da Kan Jama’a, Amma Zuwan Kwamitin Ya Ƙara Mana Ƙaimi

An ce a daren ranar Alhamis sun kunna janareta domin samar da wutar lantarki kafin su kwanta barci, ba tare da sun fahimci cewa hayaƙinsa na shiga cikin ɗakin da suke kwana ba.

A cewar mazauna yankin, hayaƙin ya mamaye ɗakin yayin da suke barci, lamarin da ya yi sanadin shaƙewarsu har suka mutu.

Wani mazaunin unguwar Farm Centre, mai suna Akong, ya ce da safiyar washegari ne aka lura janaretan har yanzu yana aiki, yayin da hayaƙi ke fitowa daga saman rufin ɗakin.

Advertisement

Ya ce maƙwabta sun yi ƙoƙarin kiran mamatan tare da buga ƙofa, amma ba a samu amsa ba. Daga bisani aka ɓalle ƙofar ɗakin, inda aka tarar da su sun mutu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an shafe kusan mako guda ba tare da wutar lantarki ba a unguwar, lamarin da ya sa mutane da dama suka koma amfani da janareta domin biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, Sunday Eitopha, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara bincike kan musabbabin mutuwar mamatan.

Lamarin ya sake tayar da hankulan jama’a kan haɗarin amfani da janareta ba tare da kiyaye matakan tsaro ba, musamman sanya shi a wuraren da hayaƙinsa zai iya shiga cikin ɗakunan kwana.

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending