News
An Kama Matashi Zai Saci Janareta A Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An cafke wani matashi a daidai lokacin da yake kokarin sace janareta a wata kotu a yankin Karamar Hukumar Ado-Odo Ota a Jihar Ogun.
Majiyarmu ta ce magatakardan kotun, Kareem Tolulope, da kansa ya damke matashin.
Yan Sandan kano cafke wasu matasa biyu da laifin yin garkuwa yara
Bayanai sun ce a ranar Talata wanda ake zargin ya kutsa cikin ofishin da aka ajiye janaretan da zummar zai yi awon gaba da shi
Aminiya ta rawaito cewar majiyar, matashin ya yi amfani da damar hutun aikin da aka bai wa ma’aikata don zuwa karbar Katin Zabensu wajen aikata laifin.
Abubuwan da aka samu a jikinsa sun hada da wata ‘yar jaka da sukundireba.
Ya zuwa hada wanna labari, an kasa samun mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, balle a ji ta bakinsa kan batun.
