News
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bayan Surfawa Shugaban Kasa Ashar
Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan zagin Shugaban Tunisiya Kais Saied da kuma yada farfaganda kan tsaro.
Mutumin da hukumomin Tunisiya suka sakaye sunansa an yanke masa hukunci kan zargin aikata laifuka guda uku da suka hada da barazanar hambarar da gwamnati wanda ke kasancewa cin amanar kasa da zagin Shugaba Saied da kuma yada labaran karya a kafafen sada zumunta.
Da yake yanke hukunci kan laifin da mutumin ya aikata, alkalin kotun ya sanar da cewa laifin da mutumin mai shekaru 51 ya aikata yaci karo da kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa kwaskwarima a 2022, musamman dokar nan mai lamba 54 da tayi hani kan yada kamalan kiyayya a Intanet.
Tun bayan hawansa kan karagar mulkin kasar ta Tunisiya, hukumomin kasar sun daure mutane da dama ciki har da ‘yan adawa da masu fafutukar kare hakkin bil Adama da manema labarai da dai sauransu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
