Connect with us

News

Mutane Da Dama Sun Mutu, Motoci Sun Kone Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Babbar Hanya

Published

on

1815ADA2 9CA4 4A0E 82D7 116B4EBDD662

Wani mummunan hatsarin tankar mai ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma konewar motocin fasinja a safiyar Juma’a, a kan titin Abeokuta–Sagamu da ke jihar Ogun.

Mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.

‎A Kama Wani Uba Yana Yunƙurin Safarar ‘Yarsa Zuwa Ƙasar Waje

Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na dare a yankin Abeokuta–Kobape–Siun–Sagamu Interchange, lokacin da wata tankar mai lita 33,000 ta kife sakamakon gudun wuce gona da iri, lamarin da ya sa ta zubar da mai a hanya kuma hakan ya haddasa gobara mai ƙarfi.

“Lamarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da kima da kuma rasa ikon sarrafa motar, wanda ya sa tankar ta kifar da kanta ta zubar da mai wanda ya haddasa gobara,” in ji Akinbiyi.

Ya kara da cewa, har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba yayin da jami’an ceto ke ci gaba da aiki a wurin.

Kungiyoyin ceto da dama sun isa wurin ciki har da jami’an TRACE, FRSC, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ogun, Nestlé Fire Service, ‘yan sanda, Amotekun, da jami’an NSCDC.

Advertisement

 

PEOPLE GAZETTE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending