Connect with us

Uncategorized

Bayan Kwana 126 A Tsare Kotu Ta Sake Dage Shari’ar El-rufai Zuwa Watan Satumba

Published

on

mallam nasir el rufai governor of kaduna state nigeria

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 22 ga watan Satumba.

El-Rufai, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da kutse a wayar tarho ba bisa ƙa’ida ba, ya shafe kwanaki 126 a tsare tun bayan kama shi a watan Fabrairu.

Advertisement

Rashin Alfanun Kafa ’Ƴansandan Jihohi Ya Fi Fa’idodinsu Yawa — Farfesa Fagge

A zaman kotun na ranar Talata, masu ƙara sun kammala gabatar da shaidunsu, yayin da lauyoyin El-Rufai suka bayyana aniyarsu ta neman kotu ta yi watsi da tuhumar saboda rashin isassun hujjoji.

Advertisement

Kotun ta kuma yi watsi da buƙatar sassauta sharuɗan belin da aka gindaya masa, bayan lauyoyinsa sun ce suna da wahalar cikawa.

Iyalan tsohon gwamnan sun ce har yanzu sun kasa samun wanda ya cika sharudan belin, lamarin da ya sa yake ci gaba da zama a tsare.

Advertisement

Kazalika, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), Afam Osigwe, ya soki tsauraran sharuɗan beli da wasu kotuna da hukumomin tsaro ke gindayawa, yana mai cewa a wasu lokutan suna hana waɗanda aka ba beli cin moriyar ’yancinsu.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending