Connect with us

Uncategorized

Jakadan Saudiyya a Najeriya da Dangote sun gana domin ƙarfafa alaƙar tattalin ariziƙi a tsakanin ƙasashen biyu

Published

on

Screenshot 20251207 0031092 750x375

Jakadan ƙasar Saudiyya a Najeriya, Yousef Al-Balawi, da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, sun gana domin ƙarfafa dangantarkar kasuwanci.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa Al-Balawi ya karɓi baƙuncin Dangote a ranar Juma’a a gidansa da ke Abuja.

Advertisement

Kungiyar PRP Vanguard Ta Yi Tir Da Taron Abuja, Ta Ce Ya Saba Da Doka

Jakadan ya tattauna kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar dangantaka ta tattalin arziƙi a tsakanin Najeriya da Saudiyya da kuma haɗa kai da juna a bangarorin daban-daban kamar na makamashi da kasuwanci da samar da kayayyakin more rayuwa.

Advertisement

Ya ce, tattaunawa ta ƙara fito da muhimmancin haɗin guiwa a tsakanin Najeriya da Saudiyya a yayin da suka mai da hankali wajen damarmaki na zuba jari.

A cewarsa, zaman ya kalli irin nasarar da Ɗangote ya samu a lokacin ziyarar da ya kai ƙasar ta Saudiyya da kuma irin damarmaki da kamfanin Dangote ya gani a ƙasar ta Saudiyya da kuma wasu damarmaki da kamfanin shi ma ya bai wa masu zuba hannun jari a Saudiyya.

Advertisement

Jakadan ya yi zaman cin abincin dare da Dangote tare da ba shi kyauta ta nuna jin daɗin ziyarar da ya kai masa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending