News
Kungiyar PRP Vanguard Ta Yi Tir Da Taron Abuja, Ta Ce Ya Saba Da Doka
Ƙungiyar PRP Vanguard Akida ta zargi wani ɓangare na jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) da yunƙurin karkatar da manufofinta daga asalin akidar kare muradun talakawa, tana mai cewa wasu ‘yan siyasa na ƙoƙarin mai da jam’iyyar wata hanya ta cimma burinsu na siyasa.
Zargin na kunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taron manema labarai da ta gudanar a Kano, wanda shugaban PRP Vanguard na ƙasa, Comrade Abdulmajid Yakubu Daudu, ya gabatar. A cikin sanarwar, ya yi kakkausar suka ga abin da ya kira “taron ƙarya” da wani ɓangare na jam’iyyar ya gudanar a Abuja, inda aka sanar da zaɓen sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Wasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
Ƙungiyar ta jaddada cewa PRP jam’iyya ce da aka assasa bisa akidar gurguzu domin kare haƙƙin talakawa, tana mai cewa ba za ta amince a karkatar da ita zuwa wata jam’iyyar jari-hujja ba.
Haka kuma, ta yi suka ga Dakta Hakeem Baba Ahmed, inda ta ce ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne, duk da cewa yana ikirarin jagorantar ta, tare da gayyatar ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyun adawa da ke fama da rikice-rikice su shiga PRP.
PRP Vanguard ta bayyana abin da ta kira “Kaduna Mafia” a matsayin wani rukuni na ajin masu mulki da ba su da alaƙa da talakawa, tana mai cewa wannan ɓangare ba ya adawa da tsarin jari-hujja da ke ƙara ta’azzara talauci a ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa batun shugabancin jam’iyyar na gaban kotu, tana mai gargadin masu sha’awar shiga jam’iyyar da su yi taka-tsantsan har sai an warware rikicin.
Dangane da batun sulhu, ƙungiyar ta ce wajibi ne a fara fayyace tushen haɗin kai, makomar akidar jam’iyyar, da kuma yadda za a tafiyar da manufofinta a faɗin ƙasa.
A ƙarshe, PRP Vanguard ta jaddada cewa har yanzu PRP ita ce “jam’iyyar talakawa,” kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano ya bayyana, tare da alƙawarin ci gaba da fafutuka domin kare akidarta da manufofinta.
