Connect with us

News

KARYEWAR GADA NA BARAZANA GA NOMA A ROGO:  Manoma Na Kira Ga Gwamnati Ta Ɗauki Matakin Gyara Kafin Damina ‎

Published

on

IMG 20260428 003458 098

Al’ummar garin Gwangwan da ke karamar hukumar Rogo a Jihar Kano sun bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta daukar matakin gyara gadar da ta lalace kafin zuwan damina, domin kauce wa karin matsalolin da suke fuskanta bara.

‎Mazauna yankin sun bayyana cewa karyewar gadar na kawo tsaiko mai tsanani ga zirga-zirga, musamman idan ruwa ya fara sauka, lamarin da ke hana mutane fita ko shiga garin cikin sauki.

Advertisement

Jakadan Saudiyya a Najeriya da Dangote sun gana domin ƙarfafa alaƙar tattalin ariziƙi a tsakanin ƙasashen biyu

‎“Babban abin da muke roko shi ne a gyara mana wannan gada kafin damina ta fara. Idan aka bari ruwa ya zo, wahalar za ta ninka,” in ji wani mazaunin yankin.

Advertisement

‎Sun kara da cewa matsalar gadar na shafar bangarori da dama na rayuwa, ciki har da kai marasa lafiya asibiti, zuwa makaranta da kuma safarar amfanin gona zuwa kasuwanni.

‎Bugu da kari, manoma a yankin sun bayyana cewa a bara sun fuskanci matsaloli matuka wajen fitar da amfanin gonarsu zuwa kasuwanni, lamarin da ya janyo musu mummunar asara, musamman a bangaren sayar da albasa.

Advertisement

‎“Mun yi asara sosai a bara saboda rashin gada. Ba mu samu damar kai amfanin gona kasuwa cikin lokaci ba, musamman albasa da ta lalace kafin a sayar,” in ji wani manomi.

‎Saboda haka, manoman sun jaddada kiran a gaggauta gyaran gadar kafin daminar bana ta sauka, domin kauce wa sake fuskantar irin wannan asara da ta gabata.

Advertisement

‎A cikin wata sanarwa, Sakataren Kungiyar Cigaban Matasan Karamar Hukumar Rogo , Malam Auwalu A. A. Daya So, ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa, yana mai cewa gyaran gadar zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin.

‎Ya kuma bukaci gwamnati da ta duba yiwuwar inganta hanyoyin da ke hada Rogo, Gwangwan, Ruwan Bago da Sundu domin saukaka harkokin noma da kasuwanci.

Advertisement

‎Al’ummar yankin sun ce suna da yakinin cewa gwamnati za ta saurari kukansu, tare da daukar matakin da ya dace kafin damina ta fara sauka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending