News
Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Rasu Bayan Wata Tirela Ta Murƙushe Su Gadar Hotoro A Kano
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Ana fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu bayan da wata tirela ta murƙushe su a Gadar Muhammadu Buhari, da ke yankin Hotoro a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne lokacin da tirelar, wacce ke kan hanyarta daga Arewa maso Gabas zuwa Kudancin Najeriya, ta kwace a ƙarƙashin gadar, inda ta kife.
An Bankaɗo Yadda Ake Amfani Da Asusun Banki Wajen Karkatar Da Kuɗin Haraji A Kano
Wani ganau ya bayyana cewa kimanin mutane 20 da kaya ne ke cikin motar a lokacin da hatsarin ya faru. Wasu daga cikinsu sun jikkata, yayin da wasu suka rasa rayukansu. Hukuma tana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da ƙoƙarin ba da agaji ga waɗanda suka
tsira.
Advertisements
