Connect with us

News

An Bankaɗo Yadda Ake Amfani Da Asusun Banki Wajen Karkatar Da Kuɗin Haraji A Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS) ta bankaɗo wasu asusun banki da ake amfani da su wajen karkatar da kuɗaɗen haraji na jihar.

Advertisement

Binciken hukumar ya gano cewa an yi amfani da waɗannan asusu na sirri wajen ɓoye kuɗaɗen haraji kafin zuwan sabon Shugaban Hukumar.

Shugaban KIRS, Dr. Zaid Abubakar, ya bayyana hakan yayin wani taro na kundin da tsare-tsaren ayyukan hukumar na shekarar 2024 da 2025 a ranar Laraba.

Advertisement

Hukumar Hisbah Ta Kama Shagon Siyar Da Giya A Kano 

Ya ce rashin bayar da cikakken rahoton kuɗin shigar da shugabannin baya suka samu ya haddasa asarar biliyoyin nairori. Saboda haka, sabuwan shugabancin KIRS ta ƙirƙiro wasu tsare-tsare don dakile zirarewar kuɗi daga hukumar.

Duk da cewa hukumar ba ta bayyana adadin kuɗin da aka karkatar ba, Abubakar ya ce wannan matsala ce da ta hana Kano gogayya da sauran jihohi a fannin tara haraji.

Advertisement

A cewarsa, sun ƙaddamar da asusun bai ɗaya da zai tabbatar da gaskiya da kuma zama tarnaƙi ga masu karkatar da kuɗaɗen haraji.

Shugaban hukumar ya jaddada cewa, duk da yawan al’ummar Kano da damar da ake da ita wajen samun kudin shiga, hukumar ta sha fama da shugabanni marasa gaskiya tsawon shekaru.

Advertisement

Sai dai a yanzu, bayan toshe duk wata kafa da ake amfani da ita wajen karkatar da kuɗin haraji, suna sa ran samun Naira biliyan 100, wanda ke sama da Naira biliyan 70 da aka yi hasashen samu a baya.

A kokarin inganta tsarin karɓar haraji, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da buƙatar sake duba dokokin haraji a jihar, wanda ake sa ran za a kammala nan da ƙarshen 2025.

Advertisement

Baya ga haka, hukumar tana aiki don wayar da kan masu biyan haraji game da ayyukanta.

 

Advertisement

 

THE GUARDIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending