News
Mutane 23 Sun Rasa Rayuka, 48 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Tirela A Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A kalla mutane 23 sun mutu, yayin da wasu 48 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a titin Kano zuwa Maiduguri, karkashin gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke Hotoro, Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon matsalar birki da wata tirela mai dauke da kaya da fasinjoji ta samu, wanda ya janyo kifewar motar.
Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Rasu Bayan Wata Tirela Ta Murƙushe Su Gadar Hotoro A Kano
A cewar Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), reshen Kano, Umar Matazu, lamarin ya afku ne da misalin karfe 9:50 na dare, a ranar 13 ga Fabrairun 2025.
Ya ce jami’an FRSC sun hanzarta zuwa wurin domin ceto wadanda suka tsira da kuma kwashe gawarwakin da suka rasu.
Kwamandan ya bayyana cewa mutane 71 ne suka tsinci kansu cikin hatsarin, cikinsu akwai yara hudu da manya 67.
“Abin takaici, mutane 23 sun rasu, yayin da wasu 48 suka samu munanan raunuka. Mun garzaya da su zuwa babban asibitin Murtala Mohammed domin samun kulawar gaggawa,”in ji shi.
