News
Ana fargabar mutuwar mutane da dama, wasu kuma sun makale a yayin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun mutu sakamakon rugujewar wani bene mai hawa biyu a babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa lamarin ya afku ne a daren ranar Laraba sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu.
Ginin yana kan titin Legas mai yawan jama’a, ƙauyen Garki, gundumar Garki II a Abuja.
Rahotanni na nuni da cewa kawo yanzu an ceto akalla mutane bakwai tare da kwashe su zuwa asibiti, yayin da wasu ke makale.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
