Connect with us

News

Wani Jirgin Sama Dauke Da Fasinjoji Ya Kauce Daga Kan Titin Sauka A Kenya

Published

on

IMG 20260424 162213 573

Wani jirgin sama dauke da fasinjoji ya kauce daga kan titin sauka a filin jirgin saman Mandera da ke arewa maso gabashin Kenya a ranar Juma’a, inda ya kutsa cikin ciyayi a gefen hanya.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa dukkan mutane 36 da ke cikin jirgin sun tsira ba tare da samun raunuka ba, kamar yadda wani jami’in harkokin sufurin jiragen sama ya bayyana.

Advertisement

KANO: Yan Bindiga Sun Kai Hari Rogo

Jirgin kirar Embraer aircraft na kamfanin EBB Air ya tashi daga filin jirgin saman Jomo Kenyatta International Airport da ke birnin Nairobi da misalin karfe 6:56 na safiya, dauke da fasinjoji 32 da ma’aikata hudu.

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa lamarin ya faru ne bayan jirgin ya zarce karshen runway din yayin sauka.

Filin jirgin saman Mandera, wanda ke kusa da iyakokin Somalia da Ethiopia, ana amfani da shi ne musamman wajen jigilar kayayyakin agaji zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira, da kuma zirga-zirgar jiragen haya na jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa.

Advertisement

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana abin da ya haddasa aukuwar lamarin ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending