Connect with us

News

Ƴansanda Sun Kama Likitan Bogi Kan Zargin Damfarar Naira 500,000 Da Sunan Samar Da Aiki

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Jami’an ’yan sanda a Jihar Kuros Riba sun kama wani mutum mai shekara 39 da ake zargi da yin aikin likita ba tare da lasisi ba, inda ya amsa cewa ya yi wa aƙalla marasa lafiya 15 magani duk da cewa bai kammala karatun likitanci ba.

Wanda ake zargin, Udeme Emmanuel Ekpeme, ya shiga hannu ne bayan wata mata mai suna Edemawan Samuel ta kai ƙorafi ga rundunar ’yan sanda cewa ya gabatar da kansa a matsayin likita tare da karɓar Naira 500,000 da sunan samar wa ’ya’yanta aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH).

An Gano Gawar Ɗalibin Jami’a A Cikin Tafkin Ruwa A Gombe

Rahotanni sun ce binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya karɓi kuɗin ne bayan ya yi alƙawarin samar da aikin, amma bai cika alƙawarin ba.

A yayin amsa tambayoyi, Ekpeme ya ce ya taɓa shiga makarantar koyon aikin likitanci amma bai kammala karatun ba. Ya ce daga baya ya sayi wasu kayan aikin gwajin lafiya domin kula da marasa lafiya, yana fatan tara kuɗin da zai koma makaranta.

Ya kuma yi iƙirarin cewa daga shekarar 2014 zuwa 2026 ya yi wa aƙalla mutum 15 magani duk da cewa ba shi da lasisin gudanar da aikin likita.

Advertisement

Haka kuma, ya amsa cewa ya karɓi Naira 500,000 daga hannun mai ƙorafin, amma ya ce ya kashe kuɗin ne wajen biyan bashin Naira 700,000 da ake binsa.

Rundunar ’yan sandan ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, bayan kammala bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending