Connect with us

News

Babban Lauyan Gwamnatin Kano Ya Halarci Bikin Yaye Ɗaliban Blazing Star International School

Published

on

IMG 20260726 WA0089 1280x700

Daga Abbas Ibrahim

 

Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Barrista Abdulkarim Kabiru Maude, ya kasance cikin manyan baƙin da suka halarci bikin yaye ɗalibai karo na uku na Makarantar Blazing Star International School da ke unguwar Farawa a Kano.

An gudanar da bikin ne a Salma Event Centre, inda ya haɗa iyaye, malamai, masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da sauran baƙi domin taya ɗaliban murnar kammala karatunsu.

Ƴansanda Sun Kama Likitan Bogi Kan Zargin Damfarar Naira 500,000 Da Sunan Samar Da Aiki

Mamallakiyar makarantar, Hajiya Zahra Usman Bakare, ta ce an kafa makarantar ne domin samar wa yara ingantaccen ilimi tare da kyakkyawar tarbiyya, ta yadda za su zama nagartattun ‘yan ƙasa masu amfani ga al’umma.

Advertisement

 

Ta kuma yaba wa mijinta, Alhaji Mustapha Sambo Hassan, kan irin goyon bayan da yake ba ta tun kafuwar makarantar, tana mai cewa gudummawarsa ta taimaka wajen bunƙasa makarantar da cimma manufofinta.

A nasa jawabin, shugaban taron, Farfesa Garba Sambo Hassan na Jami’ar Maiduguri, ya taya ɗaliban murnar kammala karatunsu tare da yi musu fatan samun nasara a matakai na gaba na neman ilimi.

Ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, yana mai jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta samu ci gaba mai ɗorewa idan ba ta ba ilimi kulawar da ta dace.

Farfesan ya kuma buƙaci iyaye su riƙa sa ido kan karatu, tarbiyya da ɗabi’un ‘ya’yansu, yana mai cewa haɗin kan gida da makaranta na taka muhimmiyar rawa wajen gina yara masu nagarta.

 

Advertisement

Bikin ya ƙayatar da mahalarta da wasannin ilimi, raye-rayen al’adu da sauran nishaɗi da ɗalibai suka gabatar. Haka kuma an ba da kyaututtuka da lambobin yabo ga ɗaliban da suka yi fice a fannin karatu da sauran ayyukan makaranta.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin akwai tsohon Manajan Darakta na Hikima Radio, Muhammad Musa Inya, Hajiya Binta Sambo Hassan, Fatima Garba Sambo da Halima Sambo Hassan, tare da sauran iyaye, ‘yan uwa da abokan arziki.

An kammala bikin da kira ga iyaye da makarantu su ci gaba da haɗa kai wajen tabbatar da yara sun samu ingantaccen ilimi da tarbiyyar da za ta amfani kansu da al’umma baki ɗaya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending