Connect with us

News

KANO: Yan Bindiga Sun Kai Hari Rogo

Published

on

Wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba suka kai a ƙaramar hukumar Rogo ta Jihar Kano ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe Tara na dare a ranar Alhamis, a ƙauyen Barbaji da ke cikin unguwar Jajaye. Maharan, waɗanda suke kan babura sun kai hari ne kan wani ɗan sintiri mai suna Alasan Yellow a gaban shagonsa.

Advertisement

Dangote Na Shirin Gina Babbar Matatar Mai A Gabashin Afirka Don Ƙarfafa Samar Da Makamashi

Kwamandan ƙungiyar Vigilante ta Rogo, Alhaji Haruna Barhaya, ya bayyana cewa maharan sun kai kimanin mutum huɗu, kuma suna ɗauke da makamai masu haɗari. Ya ce bayan harin farko, sun wuce ofishin ‘yan sintiri inda suka riƙa harbi ba tare da bambanci ba kan mazauna yankin.

Advertisement

A cewarsa, mutum ɗaya ya mutu nan take, yayin da wasu suka jikkata da raunuka daban-daban, inda a halin yanzu mutum huɗu ke samun kulawar likitoci.

Jami’an tsaro tare da ‘yan sintiri sun kai dauki cikin gaggawa, inda aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Gwarzo domin samun kulawa ta musamman.

Advertisement

Haka kuma, jami’an tsaro sun ce sun ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da kaddamar da sintiri na haɗin gwiwa da jami’an tsaro daga ƙaramar hukumar Kiru da wasu sassan Jihar Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending