Connect with us

News

JIGAWA: Uba Ya Fasa Aurar Da ‘Yarsa Ga Wani Saurayi Saboda Goyon Bayan Tinubu

Published

on

Wani uba a jihar Jigawa  ya janye daga shirin aurar da ‘yarsa ga wani saurayi, sakamakon goyon bayan da saurayin ke yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a kafafen sada zumunta.

Gidan Radiyon Sawaba ya ruwaito cewa mutumin, Malam Sani, mazaunin unguwar Yalwawa da ke Dutse, ya ɗauki matakin ne a daren da ya gabata, duk da cewa an riga an kammala shirye-shiryen ɗaura auren da aka tsara gudanarwa a yau.

Advertisement

Majiyoyi sun ce Malam Sani ya sanar da iyayen saurayin da waliyyansa cewa ba zai ci gaba da shirin auren ba, matakin da ya jefa bangarorin biyu cikin ruɗani tare da janyo hankalin al’umma.

Dattawa da masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani domin lalubo mafita, amma mahaifin yarinyar ya nace kan matsayinsa. Ya bayyana cewa saurayin bai aikata masa wani laifi kai tsaye ba, sai dai ra’ayinsa a kan harkokin siyasa ne ya sa ya yanke wannan hukunci.

Advertisement

A cewarsa, yadda saurayin ke bayyana goyon baya ga manufofin shugaban ƙasa a kafafen sada zumunta, na nuna abin da ya kira rashin tausayi da kuma ƙarancin imani, dalilin da ya sa bai ga dacewar aurar da ‘yarsa gare shi ba.

Lamarin ya haifar da muhawara a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin rushe shirin aure ba, yayin da wasu ke goyon bayan matakin mahaifin bisa hujjojin da ya bayar.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga bangaren saurayin ko iyalansa. Sai dai masu sharhi na ganin cewa lamarin na nuni da yadda siyasa ke ƙara kutsawa cikin al’amuran zamantakewa a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending