Connect with us

News

Mazauna Sheka Yar Kasuwa Sun Koka Kan Gurbataccen Muhalli, Sun Nemi Daukin Gwamnatin Kano

Published

on

IMG 8716

A Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, mazauna unguwar Sheka Yar Kasuwa a Karamar Hukumar Kumbotso sun koka kan yadda taruwar shara ke ci gaba da addabar yankinsu, lamarin da suka ce na barazana ga lafiyarsu da rayuwarsu ta yau da kullum.

‎Rahotanni daga yankin sun nuna cewa shara ta mamaye wurare da dama, inda kwari ke shawagi a kan tarkacen abinci da sauran datti, yayin da warin da ke tashi daga wurin ke hana mazauna samun isasshen numfashi. Haka kuma, ana yawan ganin beraye da wasu ƙananan halittu na yawo a cikin unguwar.

Advertisement

Shugaba Tinubu Baya So A Yi Zaɓe So Yake A Nada Shi Shugaban Kasa Kamar Yadda Ake Nada Sarki —Dino Melaye

‎Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa matsalar ta ƙara tsananta a ‘yan shekarun nan. Mallama Safiyya, daya daga cikin mazauna, ta ce: “Magudanan ruwa sun toshe, ruwa na tsayawa a gidaje, kuma datti ya mamaye ko’ina. Wannan na jefa mu cikin mawuyacin hali.”

Advertisement

‎Ita ma Hajiya Hafsat ta ce yawaitar tsutsotsi da rashin tsafta na haddasa cututtuka, musamman ga yara ƙanana da ke zaune a yankin.

‎A gefe guda, an ruwaito cewa yara masu shekaru tsakanin shida zuwa 16 na tattara shara daga wasu unguwanni makwabta domin neman abin dogaro, duk da haɗarin da ke tattare da hakan ga lafiyarsu.

Advertisement

‎Wani ɗan kasuwa a yankin, Malam Nasir, ya bayyana cewa matsalar ta shafi harkokin kasuwanci. Ya ce: “A da shara ba ta da yawa, amma yanzu ana kawo dimbin shara kullum, abin da ya sa kwastomomi suka ragu.”

‎Hukumar Tsabtace Shara ta Jihar Kano, REMASAB, ta ce tana kokarin magance matsalar ta hanyar share shara lokaci zuwa lokaci, sai dai ta danganta ƙalubalen da ake fuskanta da ƙarancin kayan aiki da kuma rashin wayar da kan al’umma.

Advertisement

‎Sai dai mazauna yankin sun bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalar, wadda suka ce na barazana ga lafiyar al’umma da tattalin arziki a yankin.

 

Advertisement

 

PRIME TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending