Politics
Tarauni 2027 : Yadda Hafizu Kawu Ya Daidaita Gasar Siyasa
Daga Abba Anwar
Da farkon farawa dai kowa ya san cewa Maigirma Hafizu Kawu, tsohon dan majalisar tarayya daga karamar hukumar Tarauni, ba matsoraci ba ne ta fuskar siyasa. Saboda yadda tsoro ya hana wasu sauka daga mukamansu a gwamnatin tarayya dan tsayawa takara a kakar zabe ta 2027, shi wannan bawan Allan akwai dalilai biyu kwarara da su ka sa bai sauka daga mukaminsa ba.
Matsayin da yake kai yanzu haka, na Hukumar Fansho ta Kasa, na babban kwamishina da yake wakiltar Arewa Maso Yamma, kuma daga jihar Kano. Da zarar ya sauka daga mukamin to lallai Kano ce ta yi asara. Dan kuwa ba lallai idan an tashi nada wani ya kasance dan Kano ba.
MTN Ya Sanar Da Dakatar Da Tsarin Bayar Da Rancen Kati Da Data
To saboda yadda yake da kishin jiharsa, ya sa ya gwammace da ya yi watsi da tasa takarar ta kashin kansa, wato takarar majalisar wakilai ta kasa. Ya zabi jiharsa sama da tasa bukatar ta kashin kansa.
Daga lokacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada shi kuma majalisar dattawa ta kasa ta tantance shi, wanda daga bisani, a ka rantsar da shi, ya sha alwashin bayar da tasa gudummawar wajen inganta harkar fansho a kasa, tare da kyautata tsare-tsare masu alfanu wajen ganin masu hakki ba a yaudare su ko an cutar da su ba.
Kamar kuma yadda shugaba Tinubu ya amince tare da yarda da Kawu, wajen rike amanar kasa, musamman karkashin tsarin cakudawa da matasa wajen harkar mulki a kasa, ta sa jama’a su ka fi karfafa masa gwuiwa wajen ganin ya tsaya kan mukamin nasa, dan alfaharin Kano da na Arewa Maso Yamma.
Shi fa Kawu ba bakon rike mukamai ba ne a matakin gwamnatin tarayya. Misali bayan kasancewarsa tsohon dan majalisar wakilai ta kasa, daga Tarauni, a shekarar 2019 zuwa 2023, karkashin jam’iyyar APC, ya taba zama mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Shi dai Kawun nan saboda jajircewa a bagaren da ya yi fice tare da tsagwaron kishin kasa, ta sa ya samu babbar lambar nan ta yabo daga gwamnatin tarayya. Wato OON. Haka nan kuma ya halarci kwas na musamman a cibiyar nan ta “National Institute of Policy and Strategic Studies,” (NIPPS), Kuru, kusa da Jos, har ya samu matsayin “mni,” wato “Member National Institute.” Sa’annan kuma ya halarci jami’a tare da yin digirinsa na farko. Daga nan kuma ya yi ta kara samun shaidar karatu a matakai daban-daban.
Duk da kasancewarsa ya na da dukkan cancantar da ake bukata wajen yin wannan takara, amman a matsayin dalilin sa na biyu, sai ya nuna cewar shi fa ya fi bukatar samun hadin kan jam’iyya da ‘yan jam’iyya. A dalilin haka ya nuna cewar shi fa ya ma janye maganar takarar sa.
Amman fa duk da haka akwai masu ra’ayin cewa, ya fi ragowar masu sha’awar neman takarar cancanta da kusanci da masu jefa kuri’a. Haka wasu ke tunani. Bayan karfinsa da tasirinsa da tsabar ayyukan cigaba da ya kawo ga Tarauni lokacin ya na dan majalisar wakilai, duk da haka ya nuna gara dai ya janye dan a samu daidaito mai amfani tare da kara karfafa yin tsaftatacciyar gasa ta siyasa a Taraunin.
Baya ga dan majalisar tarayya din mai ci a yanzu na Taraunin, wanda ban sani ba ko ya na APC din ko bai biyo gwamna APC din ba, akwai kuma, daga cikin abokan hamayyar siyasa na Kawu, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shugabanci da kishin kasa, wato Nasir Bala Ja’oji, wanda shi ma wani gwarzo ne a harkar. Sai dai babban kalubalen da a ka ce yake fuskanta, ko gaske ne ko ba gaske ba ne, shine yadda manyan ‘yan jam’iyya daga karamar hukumar, suke yi masa gangami na rashin amincewa da takarar tasa.
Duk da cewar fa shi Kawu ba zai tsaya takarar ba, amma duk da haka a halin da a ke ciki, shi wani gwarzo ne mai zaman kansa, wanda masu zabe ke neman sanin mecece alkiblarsa. Dan su bi.
Wasu dai na yada jita-jita wacce ba ta tabbata ba cewar, wai za a iya ba Ja’oji tikitin tsayawa takara daga masu ruwa da tsaki. Sai dai babban abin lura a nan shine, idan bayar da tikitin tsayawa takara, daga sama ko daga tsakiya, zai iya zama wata hanyar samun nasara da zaman lafiya, lokacin zaben ‘yan majalisar wakilai, to lallai akwai wasu wuraren da hakan ba mai yiwuwa ba ne.
Ire-iren mazabun takarar majalisar wakilai daga Kano wadanda bayar da tikitin tsayawa takara kai tsaye zai iya kawo alhairai ga APCn da kuma ‘yan jam’iyya, to ba zai wuce irin su Dala da Bichi da Tudunwada /Doguwa da karamar hukumar cikin birni ba da wasu kalilan wurare.
Wani babban abin lura shine, idan fa ba a yi hankali ba, wani zai zo daga wani waje ya dauke takarar da kuma samun nasarar takarar. Sai dai kamar yadda wasu ke da ra’ayi su ka ce yin hakan abu ne mai matukar wahala.
Duk da cewar shi fa Kawu ba zai tsaya takara ba. Amman dai zai iya yiwuwa shi da wasu abokan adawar Ja’oji za su iya kawo wani sabo ful. Ba zan ce masa raba-gardama ba. Kawai dai wani daga wata uwa duniya wanda takara ce kadai ta kawo shi jam’iyyar. Wanda a ra’ayin wasu, da a ce kuwa Ja’o’ji zai sake shiri kuma ya zo da sabbin dabarun cin nasara, to an ce lallai za a sha kwarbai da shi.
Wasu na kara da cewa bayar da tikitin takara kai tsaye daga shugabancin jam’iyya ko daga wata kafa a mazabar dan majalisar tarayya daga Tarauni, zai iya zama tarnaki wajen samun nasarar jam’iyyar ta APC a wajen. Saboda haka su ka fi ganin ya fi kamata dai a ce a yi zube-ban-kwarya lokacin zaben fitar da gwani. Wato zaben cikin gida.
Haka nan dai a ra’ayin wasu, muddin a na son ganin an samu hamayya mai ma’ana kuma tsaftatacciya a Tarauni lokacin fitar da dan takarar dan majalisar wakilai daga APC din, to, su, a nasu ra’ayin bai kamata Ja’oji ya samu goyon baya daga Kawu ba. Haka nan bai kamata Ja’oji ya dagawa duk wani dan takara da abokan hamayyarsa za su iya kawo wa daga wata uwa duniya ba.
Amman duk da haka, an yarda cewar daga cikinsu, duk wanda ya samu tikitin tsayawa takarar, to dayan ya taimaka masa wajen samun nasarar jam’iyyar. An ce jam’iyyar za a kalla, ba shi dan takarar ba.
Alamu dai sun nuna cewar, Tarauni ta na daya daga cikin kananan hukumomin da za a samu kalubale da adawa mai dan karen zafi, a zaben dan majalisar wakilai, idan Allah Ubangiji Ya kai mu lafiya.
Ni a tawa shawarar, ya kamata a ce da Kawu da Ja’oji sun yi duk mai yiwuwa wajen samun nasarar APC din a Tarauni idan lokacin ya zo. Dan kuwa dukkaninsu su biyun su na cikin na gaba-gaba daga karamar hukumar da su ka fi kowa amfanar mulkin APC, Alhamdulillah.
Anwar ya rubuta wannan daga Kano
Juma’a, 17 ga watan Afrilu, 2026
