Opinion
Hobbasar Gwamna Abba Kan Tituna Da Sabbin Gadojin Birnin Kano
DAGA ABBA ANWAR
Kamar dai yadda kowa ya sani ne, kowace gwamnati na gama wa’adin lokacin ta, ba tare da ta gama dukkan ayyukan dake gaban ta ba. Sau da yawa za ka ga idan gwamnati ta tafi, wata ta zo, za ka ga an samu wasu ayyukan da gwamnatin da ta gabata ba ta iya yi ba, ko ba ta samu yin su ba.
To haka lamarin yake kafin shigowar gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano, akwai wasu tituna masu muhimmanci a cikin kwaryar birni, wadanda gwamnatin baya ba ta samu yin su ba. Ba wai ba titunan ba ne a wuraren, a’a sai dai kawai sun lalace yadda suke jawo cunkushewar hanyoyin sufuri tare da jawo hadurra wasu lokutan.
Sanata Barau Da Hadin Kan APC a Kano
Domin a kaucewa matsalolin da ire-iren wadannan lalatattun tituna ke haifarwa, sai gwamna ya shigo da wani tsarin kula da titunan cikin birni da ya ba shi sunan, “Urban Renewal Project.”
Ta karkashin wannan shirin ne a ka samu a ka duba titunan da su ka ji jiki kuma suke kawo tare da kara cunkoson ababen hawa, ba gaira ba dalili. Amman fa hanyar da a ka fito da ita wajen tantance ire-iren titunan da za a taba, ta taimaka gaya wajen lalubo wuraren da su ka dade a dankwafe ba tare da kula yadda ya kamata ba.
Wannan fa ba kuma a maganar wasu katafaren gadoji da gwamnatin ke yi a halin da a ke ciki. Akwai katafariyar gadar Tal’udu. Da kuma daya katafariyar gadar Kofar Dan Agundi. Dukkan wadannan gadoji an yi nisa sosai a aikin. Kuma irin gadojin nan ne na, da gani ba tambaya. A nan ina maganar yadda ayyukan ke da karko da kuma kayatarwa.
Daga lokacin da a ka kammala wadannan gadoji, za kuma a ga da wace fuska ce kuma abokan adawar siyasa, masu cewa gwamna Abba bai taba kammala wani ko wasu katafaren ayyuka ba tun shigowar sa, za su kalli mutane? A nan ba fa a na maganar wasu ayyukan da a ka rigaya a ka kammala ba.
Kasancewar shi birnin Kano ya shahara wajen samun yawan zirga-zirga na ababen hawa da ma wadanda ke tafiya ba bisa ababen hawan ba, ya sa gyare-gyaren titunan da a ke yi su ka yi tasirin gaske wajen kara saukakawa al’umma wahalar sufuri a cikin birnin na Kano.
Kasancewar Kano garin kasuwanci ne, hakan ta sa an kara samun sauki da walwala wajen zirga-zirgar harkokin kasuwanci a cikin kwaryar birnin na Kano. Musamman ma da yake wasu daga cikin titunan da a ka gama gyarawa ko a ka kusa kammala gyarawa, su na da alaka ta kut-da-kut na kusanci da wasu kasuwannin namu.
A dai karkashin wancan shirin na Urban Renewal Project, gwamnatin ta Maigirma Abba, ta kammala gyaran titunan, Lodge road da Murtala Muhammad Way da Airport road da Club road da Yahaya Gusau road da Titin Sharada da sauran ire-irensu dai. Ba wai gyara titunan ba kawai, an kawata su kuma an yi musu aiki mai karko da kyawun gani.
Baya ga wadanda a ka kammala yin su, akwai kuma wadanda a halin yanzu a na kan yin nasu gyaran. Wasu an kusa kammala su. Daga cikin wadanda a ke kan aikin nasu akwai Audu Bako Way da Lamido Crescent da Sulaiman Crescent da Titin da ya kewaye kasuwar Farm Centre da Katsina road da Sabo Bakinzuwo road da Amadu Sambo road, wanda ya taso daga titin Gandun Albasa zuwa Titin Sharada.
Babban abin ban sha’awar ma shine, yadda jama’ar dake amfana da wadannan hanyoyi ke nuna farincikinsu ga wadannan gyare-gyaren da a ke yi. Tare da kara yabawa zurfin tunanin gwamnan wajen gano cewar ya kamata a sawwakawa mutane ta bangaren gyara tituna dan samun sufuri mai inganci a birnin na Kano.
Da yawa daga cikin wasu da na dan yi wani ƙwarya-kwaryar bincike a kai sun tabbatar da cewa, ba wai samar da kyawawan hanyoyin kawai ba, ai sun ma tabbatar da cewa hatta ababen hawansu sun kara samun lafiya. Saboda an fara ceto ababen hawan nasu daga kwazazzabai da su ka yi wa titunan kaca-kaca kafin wannan lokaci.
Misalin titunan Lodge road da na Sabo Bakinzuwo road wadanda daya ke jikin gidan gwamnatin jihar Kano din, da kuma dayan dake tsallaken gidan gwamnatin, ba karamin dabara a ka yi ba wajen yi musu gagarumin aikin da a ke kan yi musu. Misali, shi Lodge road an kammala gyara shi har ma an sa masa fitilu da wasu furanni masu kayatarwa. Ga magudanan ruwa na zamani da a ka yi musu.
Yanzu ba abu ne mai wahala ba idan a ka ce wanda ya dan yi yan watanni bai je Kano ba, idan ya je yanzu daidai yake da ya bata saboda yadda a ke ta kawata wurare da hanyoyi ba kakkautawa. Wannan shirin na kyautata titunan cikin birni, ya yi daidai da yadda gwamnan ke yi kuma wajen kula da wasu bangarorin na gwamnatin sa.
Wani babban abin kawatarwa kuma shine yadda a ka kara buda titunan dan su kara fadi a samu isassun hanyoyin sufuri. Ba tare da samun wani cikas ba nan gaba.
Kuma wani ma abin ban sha’awa ga wannan hobbasa da gwamna ke yi shine, tun hayewarsa kan karaga ya sha alwashin inganta bagaren sufuri a jihar. Wanda hakan ya hada da kara inganta hanyoyin sufuri din da ya hada su tituna da kuma ababan sufuri din. Wato ababan hawa na al’umma.
Anwar ya rubuto wannan ne daga Kano
Juma’a, 13 ga watan Maris, 2026
