News
Kashi 70% Na Laifuka A Kano Na Da Alaƙa Da Miyagun Ƙwayoyi —Rahoton
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar na da alaƙa da shan da kuma safarar miyagun ƙwayoyi, lamarin da ke ƙara ta’azzara rikice-rikicen daba da ake kira Fadan Daba.
Rahoton, wanda kafar PRNigeria ta ruwaito, ya nuna cewa miyagun ƙwayoyi sun zama ginshiƙi wajen ƙarfafa kungiyoyin daba da ke aikata hare-hare, faɗace-faɗace da kuma rikice-rikicen titi a sassa daban-daban na jihar.
Trump Ya Umarci A Harbe Duk Jirgin Ruwan Iran Ɗin Da Aka Gani A Hormuz
A cewar rahoton da rundunar ta tattara ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, an kama mutane 3,081 da ake zargi da aikata manyan laifuka a shekarar 2025, inda mafi yawansu ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi.
Rahoton ya kuma bayyana cewa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi na ƙara bunƙasa, tare da haddasa mace-mace, jikkata mutane da lalata dukiyoyi a faɗin jihar.
A wani sabon salo na tattara bayanai daga jama’a, rundunar ta buƙaci mazauna jihar su bayar da bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi ta hanyar wallafa lambobin waya a shafukan sada zumunta, matakin da sashen hulɗa da jama’a ƙarƙashin CSP Abdullahi Kiyawa ya jagoranta.
Sakamakon haka, an samu sunayen mutane 513 daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kano, inda wasu daga cikinsu aka ambaci sunayensu sau da dama, abin da ke nuna yadda ake da masaniya a matakin al’umma kan waɗannan ayyuka.
Majiyoyin ‘yan sanda sun ce ana ci gaba da tantance sunayen domin ɗaukar matakan doka.
Rahoton ya ce yawan bayanan da jama’a suka bayar na nuna ƙarin shirinsu na taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalar.
Sai dai an yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, matsalar na iya ƙara tsananta tare da barazana ga tsaron jama’a.
Binciken ya kuma nuna cewa kungiyoyin daba na samun tallafi daga hanyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi, waɗanda ke ba su kuɗi da kayan aiki.
Domin magance matsalar, rundunar ta ba da shawarar kafa rundunar haɗin gwiwa da za ta haɗa da Nigeria Police Force da National Drug Law Enforcement Agency da sauran hukumomin tsaro.
An ce rundunar za ta mayar da hankali wajen kamo masu safarar miyagun ƙwayoyi da rusa hanyoyin da suke bi wajen gudanar da ayyukansu.
Sai dai rahoton ya jaddada cewa matakan tsaro kaɗai ba za su wadatar ba, inda ya buƙaci wayar da kai ga jama’a, da samar da shirye-shiryen gyaran hali ga masu shaye-shaye, tare da haɗin gwiwar shugabannin al’umma.
Masana tsaro sun kuma nuna cewa haɗuwar matsalar shan miyagun ƙwayoyi da rashin aikin yi a tsakanin matasa na ƙara haddasa rashin tsaro.
Wani masani daga Centre for Crisis Communication, Mukhtar Yau Madobi, ya ce shan miyagun ƙwayoyi ya wuce zama matsalar lafiya kawai, inda ya koma babban abin da ke haddasa rashin tsaro a Kano.
Yayin da ake fuskantar ƙaruwa a laifuka da rikice-rikicen matasa, ana ganin matakan da za a ɗauka a yanzu za su taka muhimmiyar rawa wajen daidaita al’amura a jihar.
