News
An Dakatar Da Malamai A Polytechnic Kan Zargin Sayar Da Handout
Hukumar gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi (Kogi State Polytechnic), Lokoja, ta dakatar da malamai bakwai daga aiki bisa zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da sayar da handout da littattafai ba tare da izini ba, da kuma zargin neman lalata da ɗalibai.
Mai magana da yawun kwalejin, John Onimisi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Trump Ya Dakatar Da Kai Wa Iran Hari Saboda Karancin Makamai — Rahoto
A cewarsa, malamai shida an dakatar da su ne tun ranar 22 ga Yuli, 2026, bayan an zarge su da sayar da handout da littattafai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da aka dakatar da wani malami guda saboda zargin neman lalata da ɗaliba.
Ya ce, baya ga dakatarwar, hukumar makarantar ta kuma fara gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da suka haɗa da neman lalata domin ba da maki, ayyukan ƙungiyoyin asiri (cultism) da sauran laifukan rashin ɗa’a da ake zargin suna faruwa a harabar makarantar.
Wasu majiyoyi a makarantar sun yi zargin cewa wasu malamai na neman lalata ko kuɗi daga hannun ɗalibai mata domin ba su maki masu kyau a jarabawa.
Majiyoyin sun kuma ce ana zargin ayyukan ƙungiyoyin asiri sun sake bayyana a makarantar, tare da cewa matakan ladabtarwa da aka kafa a gwamnatin da ta gabata sun yi rauni, lamarin da ya bai wa wasu ma’aikata da ɗalibai damar aikata abubuwan da suka saɓa wa ƙa’ida.
Haka kuma, an yi zargin cewa ɗalibai mata da ke kai ƙorafin cin zarafi ba sa samun isasshen kariya daga makarantar, yayin da ake fuskantar su da tsangwama.
Sauran zarge-zargen sun haɗa da sake komawar tilasta wa ɗalibai sayen handout, da sakaci wajen tabbatar da sanya kayan makaranta da amfani da katin shaidar ɗalibai, lamarin da ake zargin ya janyo raguwar ɗa’a a harabar makarantar.
Da yake mayar da martani, Onimisi ya ce mahukuntan makarantar sun miƙa dukkan zarge-zargen ga kwamitin ladabtarwa domin gudanar da cikakken bincike.
Ya tabbatar da cewa za a sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala shi, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi.
