News
Dakarun Soji Sun Cafke Jami’insu Kan Zargin Kai Wa ‘Yan Ta’adda Kayan Aikin Soji
Dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wani soja da ake zargi da hannu wajen kai wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kayan aikin soja da kayan sawa na rundunar, a wani mataki da ake ganin zai ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin, Private Mohammed Yusuf, mai lamba 23NA/84/1939, wanda ke aiki a Nigerian Army Ordnance Training Facility (NAOTF) da ke Legas, a ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a Jidari Bus Stop da ke Maiduguri.
An Dakatar Da Malamai A Polytechnic Kan Zargin Sayar Da Handout
Rahotannin sun ce sojan ya kasance cikin jerin waɗanda Rundunar Sojin Najeriya ke nema, bayan zargin cewa ya bar wurin aikinsa ba tare da izini ba, sannan ya isa Maiduguri tun ranar 7 ga Yuli, 2026, inda ake zargin ya buya.
Binciken farko ya nuna cewa an kama shi ne yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar Kamaru domin guje wa jami’an tsaro.
Haka kuma, majiyoyin tsaron sun ce ana zargin wani soja, Private Baba Kamal Sale, mai lamba 25NA/89/12687, daga Corps of Intelligence da ke Dikwa, da ba Mohammed Yusuf mafaka a unguwar Gomari Costain da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno.
Bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an 7 Provost Group sun sanya wanda ake zargin ƙarƙashin sa ido na tsawon sa’o’i 24 kafin daga bisani su yi nasarar cafke shi ba tare da wata tangarda ba.
A halin yanzu, ana tsare da Mohammed Yusuf a hedikwatar 7 Provost Group, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da ake masa na kai wa ‘yan ta’adda kayan aikin soja, tare da ƙoƙarin gano ko akwai wasu da suka haɗa baki da shi.
Majiyoyin tsaro sun bayyana kamen a matsayin wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin da Rundunar Sojin Najeriya ke yi na dakile duk wani yunkuri na taimaka wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga cikin jami’an tsaro, tare da tabbatar da cewa duk wanda bincike ya kama da hannu zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
