News
Gwamnatin Bauchi Ta Musanta Rahoton Kayyade Sadakin Budurwa zuwa ₦3,000 Da Na bazawara zuwa ₦1,500
Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da kayyade sadakin budurwa zuwa ₦3,000 da na bazawara zuwa ₦1,500, tana mai bayyana batun a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a.
Rahotannin, da suka bazu musamman a shafukan Facebook da TikTok, sun yi zargin cewa gwamnatin jihar ta fito da sabon tsarin kayyade sadaki, tare da cewa Sarkin Sayawa (Gum Zar) ya umarci al’ummar yankinsa su bi tsarin.
An Dakatar Da Malamai A Polytechnic Kan Zargin Sayar Da Handout
Haka kuma, wani saƙo da aka wallafa a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa sadakin budurwar da ta taɓa haihuwa ba tare da aure ba zai kasance ₦3,000, yayin da wasu mata marasa aure za a aurar da su ba tare da an biya sadaki ba.
Sai dai da yake magana da manema labarai a Bauchi ranar Asabar, Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Bauchi, Injiniya Muhammad Binni Abdulkadir, ya karyata waɗannan ikirari baki ɗaya, yana mai cewa ba su da tushe kuma wasu ne suka ƙirƙire su domin tayar da ruɗani a tsakanin al’umma.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta taɓa ƙirƙiro ko amincewa da wata manufa da ta shafi kayyade sadakin bazawara, budurwa ko wata mace ba, yana mai jaddada cewa gwamnatin ba ta da wata irin wannan tsari.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da jita-jitar, tare da gujewa yaɗawa ko amincewa da duk wani bayani da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, domin kauce wa haddasa ruɗani da rashin fahimta a tsakanin jama’a.
Ya kuma tabbatar da cewa tun bayan hawansa mulki, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya ci gaba da mutunta koyarwar addinin Musulunci, al’adun gargajiya da kyawawan ɗabi’un al’ummar Jihar Bauchi, yana mai cewa gwamnatin sa ba za ta ɗauki wani mataki da zai saɓa wa waɗannan ƙimomi ba.
