Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Miyagun Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Kai Naira Biliyan 10 A Legas

Published

on

images (1)

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta sanar da kama ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 10 a tashar ruwan Legas, tare da kame wasu manyan dilolin ƙwaya.

NDLEA ta kuma bayyana nasarar ƙwato alburusai 401 a jihohin Kaduna da Kaduna, baya ga wasu tarin ƙwayoyi da aka shirya safararsu zuwa Birtaniya.

Trump Ya Dakatar Da Kai Wa Iran Hari Saboda Karancin Makamai — Rahoto

Wata ƴar kasuwa mai shekaru 55 ce ta ɓoye hodar iblis a cikin kayan abinci wadda nauyinta ya kusa kilogram 4 domin safararta zuwa Birtaniya.

Haka zalika, bayan ƙwace ƙwayoyin da aka yi mata safararsu daga Amurka, NDLEA sun yi ram da wata matashiyar ƴar kasuwa Emmanuella Chukwu-Edo.

Wannan dai na ƙunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi ya fitar yau Lahadi, mai ƙunshe da bayanai kan mabanbantan nasarorin da hukumar ta samu a ƴan kwanakin nan.

Advertisement

Shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya yabawa jami’ansu na jihar Legs da Edo da Kaduna da Katsina, bisa jajircewar da sukai har aka samu wannan nasara, tare da ƙara yin kira dasu mayar da hankali kan muradunsu na yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi.

 

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending