Politics
Takara a ADC: An Kayyade Shekaru 55 a Matsayin Iyaka Ga ‘Yan Siyasa —Nafi’u Bala
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar haɗaka ta ADC a Najeriya ta sanar da cewa ba za ta amince da ‘yan takara masu shekaru sama da 55 ba a duk wata gasa ta siyasa a ƙarƙashinta, matakin da ta ce na da nufin bai wa matasa dama su taka rawa a shugabanci.
Wani jigo a jam’iyyar kuma mai ikirarin shugabancin ta na ƙasa, Nafi’u Bala, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Sashen Hausa na BBC Hausa.
Nafi’u Bala ya ce Najeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa, yana mai danganta hakan da yadda ake ci gaba da bai wa dattijai masu shekaru masu yawa damar riƙe madafun iko a siyasa.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a bai wa matasa dama domin su gwada kwarewarsu da basirarsu a harkokin dimokuraɗiyya da mulki, yana mai jaddada cewa hakan na iya taimakawa wajen samar da sauyi mai ma’ana a ƙasar.
Sanarwar na zuwa ne a yayin da ake fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyar ADC, tsakanin ɓangaren Nafi’u Bala da kuma na David Mark, inda kowanne ke iƙirarin shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
