News
Cikar Oluremi Tinubu Shekaru 66 Alheri Ne Ga Wa’adin Shugaba Tinubu Na Biyu – Kwankwaso
Daraktan Gudanar da Kuɗi na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are, Dr Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana cikar shekaru 66 da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi a matsayin wata alama ta alheri ga ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Dr Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yayin da yake taya Uwargidan Shugaban Ƙasar murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Yara ’yan kasa da shekaru 13 sun fafata a gasar kwallon kafa da kamfanin Milo ya shirya a Kano
Ya bayyana Oluremi Tinubu a matsayin ’yar Najeriya mai kishin ƙasa, wadda ta bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa, dimokuraɗiyya da kuma tallafa wa al’umma.
A cewarsa, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kasance tana halartar wuraren da ake buƙatar taimako, bukukuwa da kuma lokutan alhini, abin da ya ce ke nuna kulawarta da halin da ’yan Najeriya ke ciki.
Dr Kwankwaso ya ce ayyukan jin ƙai da tallafa wa al’umma da Oluremi Tinubu ke yi sun fara tun kafin ta zama Uwargidan Shugaban Ƙasa.
Ya bayyana cewa a lokacin da take Uwargidan Gwamnan Jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007, ta kafa gidauniyar New Era Foundation, wadda ta tallafa wa mata, yara da matasa.
Ya kuma yi nuni da tallafin naira miliyan 20 da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayar ga wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani, yana mai cewa hakan ya nuna irin goyon bayanta ga ci gaban matasa da haɗin kan ’yan Najeriya.
“Mun taya Mai Girma Uwargidan Shugaban Ƙasa murnar zagayowar ranar haihuwarta, kuma muna tabbatar mata cewa za mu haɗa kai domin ganin mahaifinmu, mijinta mai daraja, Shugaba Tinubu, ya samu damar komawa ofis karo na biyu,” in ji Dr Kwankwaso.
