News
Matashi Ya Hallaka Abokinsa Kan Yawan Tashinsa Sallar Asuba A Kano
An gurfanar da wani matashi mai suna Ayuba Isa a Babbar Kotun Jihar Kano da ke Audu Bako Secretariat, bisa tuhumarsa da kashe abokinsa, Ibrahim Dan Larai, saboda yawan tashinsa domin su tafi Sallar Asuba a garin Tumfafi, karamar hukumar Dawakin Tofa.
Bayanan da aka gabatar a kotu sun nuna cewa lamarin ya faru ne a bara, lokacin da rikici ya barke tsakanin matasan biyu kan yawan tashi da Ibrahim ke yi wa Ayuba domin su tafi masallaci. Rikicin ya jawo fushi ga Ayuba, har ya kai ga caka wa abokin nasa wuƙa a wuya, inda ya mutu nan take.
Fiye Da Musulmi 4,700 Suka Mutu A Rikice-rikicen Da Suka Auku A Filato — JCDA
A zaman kotun da aka yi ranar Alhamis, lauyan gwamnati, Barrister Amina Uba, ta kira shaidu biyu — ASP Cindu Cuwa da Inspector Buhari — waɗanda suka bayyana yadda suka gudanar da bincike kan kisan. Wannan ya ƙara jimillar shaidun da gwamnati ta gabatar zuwa uku.
Bayan sauraron shaidu uku a zaman na yau, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta ɗage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Janairu, 2026.
