Connect with us

News

2027: Za Mu Ci Gaba da Haska Ayyukan Alherin Ja’o’ji a Tarauni – Babaleliya

Published

on

20260618 204217 COLLAGE

Wani jigo a siyasar Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Abubakar Abdullahi Babaleliya Unguwa-Uku, ya jaddada kudurinsa na ci gaba da bayyana ayyukan alheri da kyawawan manufofin ci gaba na Hon. Nasir Bala Aminu Ja’o’ji domin tabbatar da nasararsa a babban zaben shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Babaleliya ya fara da gode wa Allah Madaukakin Sarki tare da nuna godiyarsa ga al’ummar Karamar Hukumar Tarauni bisa addu’o’i da goyon bayan da suke bai wa Hon. Nasir Bala Aminu Ja’o’ji.

Advertisement

Ya bayyana Ja’o’ji a matsayin shugaba mai kishin jama’a wanda ayyukan alherinsa suka bazu a sassan Karamar Hukumar Tarauni da ma Jihar Kano baki daya.

“Hon. Nasir Bala Aminu Ja’o’ji mutum ne da ayyukan alherinsa suka mamaye lungu da sakon Tarauni. Hatta masu adawa da shi a siyasa kan yaba da irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma,” in ji shi.

Advertisement

Babaleliya ya kara da cewa shi da abokan tafiyarsa za su ci gaba da wayar da kan jama’a kan ayyukan ci gaba da gudummawar da Ja’o’ji ke bayarwa domin tabbatar da cewa al’umma sun fahimci irin rawar da yake takawa wajen bunkasa yankin.

Ya ce za su ci gaba da sadaukar da lokacinsu, karfinsu da dukiyarsu wajen tallata manufofi da ayyukan da suka yi imanin za su kawo ci gaba ga al’ummar Tarauni.

Advertisement

A cewarsa, wannan kokari na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da nasarar Hon. Nasir Bala Aminu Ja’o’ji a matsayin wakilin Karamar Hukumar Tarauni a babban zaben kasa da za a gudanar a shekarar 2027.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending