Connect with us

News

Shigar Malamai Siyasa Ya Fi Zama Ana Yi Wa ‘Yan Siyasa Addu’a  — Sheikh Gumi

Published

on

FB IMG 1785756611870 747x420

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa babu wani laifi idan malaman addini suka shiga siyasa tare da neman mukamai, yana mai cewa hakan ya fi amfani fiye da zama ana yi wa ‘yan siyasa addu’a daga gefe.

Malamin ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, yayin da ake ci gaba da muhawara kan ko ya dace malamai su tsaya kan wa’azi da karantarwa kawai ko kuma su shiga siyasar jam’iyyu domin taka rawa a harkokin mulki.

Mahaifiyata Ta Riƙa Sayar Da Koko Da Kosai Domin Gina Rayuwarmu — Christopher Musa

Muhawarar ta ƙara ɗaukar hankali ne bayan wasu fitattun malaman addinin Musulunci suka bayyana aniyarsu ta shiga siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Daga cikin malaman da lamarin ya shafa akwai tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, da kuma malamin addini na Sakkwato, Bashir Ahmad Sani, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027.

Masu adawa da shigar malamai cikin siyasa na ganin cewa siyasa na tattare da rarrabuwar kawuna, zarge-zarge da cin mutunci, lamarin da ka iya shafar martabar malamai da tasirinsu a cikin al’umma.

Advertisement

Sai dai masu goyon bayan wannan ra’ayi suna cewa bai kamata malamai masu ilimi da nagarta su tsaya a gefe ba, alhali ƙasar ke fuskantar ƙalubalen shugabanci. A cewarsu, ya dace su shiga siyasa domin ba da gudunmawa kai tsaye wajen tafiyar da mulki.

Da yake bayyana matsayinsa kan batun, Sheikh Gumi ya ce shiga siyasa da fuskantar ƙalubalenta ya fi zama ana yi wa ‘yan siyasa addu’a daga waje.

Ya ce, “Malamin addinin da ya shiga siyasa kuma ya jure wahalhalunta ya fi wanda yake zaune kan tabarmar sallah yana yi wa ‘yan siyasa addu’a.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending