News
Mahaifiyata Ta Riƙa Sayar Da Koko Da Kosai Domin Gina Rayuwarmu — Christopher Musa
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta kasance tana sayar da koko da kosai domin tallafa wa iyalansu, yana mai cewa irin wannan ƙoƙari ne ya zama tubalin nasararsa a rayuwa.
Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taron horaswa da ƙarfafa gwiwa ga zawarawa da matan jami’an tsaro da aka gudanar a Abuja.
IIIT Ta Horar da Mata ‘Yan Jarida kan Amfani da Kafafen Yaɗa Labarai Wajen Gina Al’umma
A cewarsa, bai kamata a raina ƙananan sana’o’i ba, domin sana’ar da mahaifiyarsa ta yi ta taimaka wajen kula da iyalansu da kuma ba shi damar samun ilimi da cimma burinsa har ya kai ga zama Ministan Tsaro.
Ya ce yana alfahari da irin sadaukarwa da jajircewar mahaifiyarsa, yana mai jaddada cewa kowace sana’a ta halal tana da daraja kuma tana iya zama hanyar samun nasara.
Ministan ya kuma yi kira ga matasa da mata su rungumi sana’o’in hannu da dogaro da kai, yana mai cewa darajar mutum ba ta ta’allaka da irin aikin da yake yi ba, illa dai yadda yake gudanar da shi cikin gaskiya da riƙon amana.
