Connect with us

News

Majalisar Dokokin Kano Ta Haramta Makarantu Masu Zaman Kansu Ƙara Kuɗin Makaranta Sama Da Kashi 10

Published

on

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Zaben Kananan Hukumomin Da Aka Shirya Yi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da gyaran dokar da ta haramta wa makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da bin ƙa’idojin da doka ta tanada ba, tare da gindaya cewa duk wani ƙari ba zai wuce kashi 10 cikin 100100 na kuɗin makarantar da ake biya ba.

Sabuwar dokar, mai suna Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai (Gyara) ta 2026, ta tanadi sabbin matakan da za su ƙarfafa sa ido kan ayyukan makarantu masu zaman kansu tare da kare haƙƙin iyaye daga ƙarin kuɗin makaranta ba bisa ƙa’ida ba.

Shigar Malamai Siyasa Ya Fi Zama Ana Yi Wa ‘Yan Siyasa Addu’a  — Sheikh Gumi

Majalisar ta amince da dokar ne a zaman da ta gudanar ranar Litinin, bayan da Magatakardan Majalisar, Bashir Diso, ya karanta rahoton kwamitin da ya tantance kudirin.

Da yake bayani bayan amincewa da dokar, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya ce gyaran dokar ya wajabta wa dukkan makarantu masu zaman kansu na firamare da sakandare tuntuɓar Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) kafin aiwatar da duk wani ƙarin kuɗin makaranta.

Ya bayyana cewa dokar ta kuma kayyade cewa ƙarin kuɗin makaranta ba zai wuce kashi 10 cikin 100 na kuɗin da ake biya a halin yanzu ba.

Advertisement

Haka kuma, dokar ta haramta wa makarantu masu zaman kansu karɓar kuɗaɗen jarrabawa daga ɗalibai fiye da adadin kuɗin da hukumomin shirya jarrabawa irin su WAEC, NECO da NBTE suka kayyade.

Bugu da ƙari, gyaran dokar ya rage kuɗin rajista da makarantu masu zaman kansu ke biya Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100.

Dokar ta kuma tanadi cewa Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu zai kasance tsohon ma’aikacin gwamnati ko ƙwararren masanin harkar ilimi da ya kai aƙalla mataki na 14 a aikin gwamnati.

A cewar Lawan Hussaini, waɗannan gyare-gyare na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta tsarin gudanar da makarantu masu zaman kansu da kuma tabbatar da samun ingantaccen ilimi a faɗin Jihar Kano.

Dokar na jiran sahalewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kafin ta fara aiki a hukumance..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending