News
Gwamnatin Tarrayya Ta Musanta Shirin Soke NBAIS
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa na shirin soke Hukumar Kula da Jarabawar Larabci da Ilimin Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS).
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a ta ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Laraba a Abuja, ta bayyana cewa ikirarin ba gaskiya ba ne, kuma babu wata hujja da ke nuna hakan.
Ta ce ma’aikatar ba ta gabatar da wata doka a gaban Majalisar Dokoki ta Kasa domin soke NBAIS ba, kuma ba ta amince da wata manufa da za ta tauye ayyukan hukumar ba.
Boriowo ta yi gargadin cewa irin wannan bayanan ƙarya na iya haifar da fargaba da rudani a tsakanin ɗalibai, iyaye, malamai, ƙungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki.
Ta jaddada cewa NBAIS har yanzu hukuma ce da gwamnatin Najeriya ta amince da ita wajen gudanar da jarabawa da bayar da takardun shaida a cikin tsarin ilimin ƙasar.
Ma’aikatar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin ilimi da aka kafa bisa doka, tare da bin manufofin ilimi na ƙasa da ka’idojin adalci da bai wa kowa dama iri ɗaya.
A ƙarshe, ma’aikatar ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton, tare da neman su rika dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati domin samun ingantattun bayanai kan manufofi da sauye-sauyen da suka shafi ilimi.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
