News
Ƙungiyar Tsofaffin Dalibai Ta Nemi A Gaggauta Sake Buɗe Unity College Karaye Aka Rufe Sama Da Shekaru Uku
Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Haɗaka ta Karaye (KAROBA) ta sake jaddada aniyarta na ganin an sake buɗe Kwalejin Haɗaka ta Karaye (Unity College, Karaye), wadda aka rufe fiye da shekaru uku da suka gabata sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙungiyar ta Ƙasa, Kwamared Ibrahim Salihu Kurna, ya fitar bayan kammala babban taron haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Gudanarwar KAROBA ta Ƙasa da mambobin kwamitocin Babban Taron Shekara-shekara (AGM), wanda aka gudanar a ranar 14 ga Yunin 2026 a Sakatariyar Ƙungiyar ta Ƙasa.
An Kama Mutum Takwas Saboda Yada Labaran Karya A Najeriya
Sanarwar ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka shafi bunƙasa ilimi, inganta walwalar mambobi, da kuma ƙarfafa tasirin ƙungiyar a cikin al’umma.
A cewar Kurna, mahalarta taron sun yi nazari kan rahoton AGM na baya-bayan nan, inda suka tattauna nasarorin da aka samu, ƙalubalen da aka fuskanta da kuma hanyoyin magance matsalolin da har yanzu ke bukatar kulawa.
Ya ce an kuma tattauna dabarun inganta shirye-shiryen tarukan AGM na gaba domin tabbatar da samun gagarumar halarta da kuma cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Dangane da harkokin gudanarwa da abubuwan more rayuwa, KAROBA ta tabbatar da kammala yarjejeniyar kuɗi domin biyan kuɗin hayar Sakatariyar Ƙungiyar ta Ƙasa na shekara guda. Haka kuma, shugabannin ƙungiyar sun fara tattaunawa kan samar da sakatariya ta dindindin da za ta zama cibiyar gudanarwa da kuma abin tunawa ga ƙungiyar.
Sai dai batun da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne ci gaba da fafutukar sake buɗe Unity College Karaye, wadda gwamnatin da ta gabata ta rufe saboda matsalolin tsaro.
Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta ƙara ƙaimi wajen tattaunawa da hukumomin gwamnati, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da yanayin da zai ba da damar sake buɗe makarantar cikin aminci tare da dawo da harkokin karatu yadda ya kamata.
“Wannan taron ya sake nuna jajircewar KAROBA wajen kare muradun mambobinta da kuma tabbatar da farfaɗo da makarantar da ta yi tasiri wajen tarbiyya da ilimantar da dubban ɗalibai,” in ji Kurna.
Ya ƙara da cewa tsawaita rufe makarantar na ci gaba da tayar da hankali ga tsofaffin ɗalibanta da al’ummar yankin, don haka ƙungiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman mafita mai ɗorewa.
KAROBA ta bayyana fatan cewa, ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, za a sake buɗe Kwalejin Haɗaka ta Karaye nan gaba kaɗan domin ta ci gaba da bayar da gudunmawarta wajen bunƙasa ilimi da gina makomar matasa a jihar Kano.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
