News
Fiye Da Musulmi 4,700 Suka Mutu A Rikice-rikicen Da Suka Auku A Filato — JCDA
Ƙungiyar Jasawa Community Development Association (JCDA) ta ce fiye da Musulmi 4,700 ne suka rasa rayukansu a rikice-rikicen da suka auku a Jihar Filato cikin shekaru 25 da suka gabata.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Yawale Muhammad ne, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da aka yi a Masallacin Juma’a na Jos, yayin bukukuwan tunawa da wadanda suka mutu a rikice-rikicen da suka auku jihar.
A cewar JCDA, an tattara adadin mutanen da aka kashe ta hanyar bincike da rubuta takardun shaida na hare-haren da suka faru a sassa daban-daban na jihar.
Rikicin 2001 ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 700.
A 2002, a harin Eto Baba, daruruwan Musulmi ne aka kashe.
Rikicin Yelwa-Shendam na 2004 ya yi ajalin akalla mutane 700.
Rikice-rikicen bayan zabe na 2008 sun hallaka fiye da 1,000.
Hare-haren 2010 da suka shafi Dutse Uku, Gero da Kuru Jenta sun yi sanadin fiye da mutane 2,000.
A 2011, mutum 20 aka kashe a filin Idi na Rukuba Road.
A 2021, daruruwan matafiya Musulmi da ke kan hanyar dawowa daga gaisuwar ga Sheikh Dahiru Bauchi sun rasa rayukansu a Rukuba Road.
A 2025, Musulmi 14 daga Zariya da ke kan hanyar zuwa bikin aure a Mangu aka kashe.
“Shugaban kungiyar ya ce:“28 ga Nuwamba rana ce da suka warewa domin tunawa da munanan rikice-rikicen da suka taba faruwa a Matsayin Ranar jimami ce, ta addu’a da tunani.”
Ya kara da cewa ba nufinsu ba ne kawo tashin hankali, sai dai tabbatar da cewa gaskiya ta zauna a tarihi.
