News
Kotu Ta Yanke Wa Dalibi Hukuncin Kisa Kan Zargin Kashe Budurwarsa
A Jihar Ribàs, Babbar Kotu da ke Fatakwal ta yanke wa wani dalibin Jami’ar Fatakwal hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da ta samu hujjojin da suka tabbatar da cewa ya kashe budurwarsa.
Rahotanni daga kotun na cewa dalibin, wanda ke karatu a Sashen Injiniyan Sinadaran Man Fetur a lokacin da abin ya faru, ya kashe budurwar tasa mai aji uku a gidansa da ke unguwar Mgbuoba, a Karamar Hukumar Obio-Akpor.
Fiye Da Musulmi 4,700 Suka Mutu A Rikice-rikicen Da Suka Auku A Filato — JCDA
Bayan kisan, an ce ya yanke gawarta sannan ya sanya a cikin tirelolin (wheelbarrow) da nufin zubar da ita, sai dai jami’an tsaro suka cafke shi.
Yayin yanke hukunci, Mai Shari’a Chinwe Nsirim-Nwosu ta ce masu gabatar da kara sun gamsar da kotu cewa wanda ake tuhuma shi ne ya aikata laifin. Ta kara da cewa kotun ta samu tabbacin cewa da gangan ya shirya har ya aiwatar da kisan, wanda hakan ya sa aka yanke masa hukuncin kisa.
