Connect with us

News

Kotu Ta Ƙwace Filayen Rukunin Gidajen Goodluck Jonathan Masu Darajar Biliyoyin Naira

Published

on

kotu

Kotu ta  ƙwace filaye Masu darajar biliyoyin naira da aka ware domin aikin rukunin gidajen Goodluck Jonathan Legacy Model Housing Estate zuwa Gwamnatin tarayya.

Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace filayen ƙasa masu darajar biliyoyin naira da aka ware domin aikin rukunin gidajen Goodluck Jonathan Legacy Model Housing Estate zuwa Gwamnatin tarayya.

Advertisement

Babban Hafsan Sojojin Libiya Ya Rasu A Hadarin Jirgin Sama A Turkiyya

Mai shari’a Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan amincewa da buƙatar da hukumar ICPC ta gabatar, wadda ba a yi adawa da ita ba.

Kotun ta umurci ICPC, tare da haɗin gwiwar babban bankin bada lamunin gidaje na Najeriya (FMBN), da su kula da kammala ginin gidaje 962 da aka tsara tun farko.

Advertisement

A hukuncin, kotun ta ƙwace Filaye Lamba 4 da 5 da ke Kaba District, Abuja, waɗanda darajarsu ta kai sama da ₦5 biliyan, bisa zargin cewa sun samo asali ne daga haramtacciyar hanya.

Kotun ta kuma umarci a miƙa kadarorin ga FMBN, wanda aka bayyana a matsayin wanda abin ya shafa.

Advertisement

 

Kotun ta kuma ba da umarnin kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin ICPC da FMBN domin kammala aikin ginin da tabbatar da amfanin gidajen ga jama’a.

Advertisement

 

An rawaito cewa aikin, wanda aka fara a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya samu kuɗi dala miliyan 65 daga FMBN, amma ba a gina gida guda ɗaya ba kafin shigar ICPC cikin lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending