News
”Ya Kamata A Canza Salon Yadda Ake Yakar Ta’addanci A Najeriya”
Farfesa Usman Yusuf ya yi kira da a sauya salon yaƙar ta’addanci a Najeriya, yana mai cewa dogaro da ƙarfin soja kaɗai tsawon shekaru 12 bai kawo ƙarshen ‘yan fashin daji ba.
Ya jaddada cewa matsalar ta samo asali ne daga gazawar shugabanci, talauci, rashin adalci da rugujewar zamantakewa, tare da buƙatar tattaunawa, sulhu da saka shugabannin gargajiya da na addini cikin mafita.
FRSC Ta Tura Ƙarin Jami’ai Kan Hanyar Abuja–Lokoja Bayan Cunkoson Motoci Na Kwanaki Biyu
A cewarsa, martanin gwamnatocin jihohi da ta tarayya tsawon wadannan shekaru ya ta’allaka ne kan kara amfani da karfin soja, lamarin da ya haifar da mummunan sakamako.
Ko da yake ya amince cewa sojoji na da rawar takawa, Farfesa Yusuf ya jaddada cewa ba za a taba samun cikakkiyar nasara ta hanyar soji kadai ba.
Ya ce a tarihin duniya, irin wadannan rikice-rikice ba a taba warware su a filin daga kawai ba.
Ya kara da cewa dukkan matsalolin suna da tushe a cikin al’umma, don haka hanyoyin magance su ma dole ne su fito daga al’umma.
Ya ce manyan tsare-tsare daga Abuja ba tare da shigar da shugabannin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki na cikin gida ba, sun gaza tsawon shekaru 12, kuma ba za su taba yin nasara ba.
