News
Gwamnan Gombe Ya Kori Hadimansa 4 Kan Cin Zarafin Kansila
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kori wasu hadimansa hudu nan take bayan samun su da hannu a cin zarafin wani a jihar.
Kansilan da lamarin ya shafa shi ne Abdulrahman Abubakar Sheriff, Dan Buba wanda ke wakiltar Mazaɓar Shamaki da ke Ƙaramar Hukumar Gombe.
”Ya Kamata A Canza Salon Yadda Ake Yakar Ta’addanci A Najeriya”
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa korar ta fara aiki nan take, tare da umartar waɗanda aka sallaman da su mika duk wani kayan gwamnati da ke hannunsu ga hukumar da ta dace ba tare da ɓata lokaci ba.
Babban Daraktan Yada labarai na gidan gwamnatin Isma’ila Uba Misilli ya sanar cewa rahoton da hukumomin tsaro da kwamitin bincike na musamman da gwamnatin jihar ta kafa kan lamarin, sun tabbatar da rawar da waɗannan hadimai suka taka a cikin lamarin, shi ya sa gwamnan ya sallame su.
Hadiman da aka kora sun hada da
Sauran sune Rabiu Sulaiman Abubakar, mai taimakawa gwamna na II kan Kafofin Sadarwa na Zamani da Ali Ibrahim Baban Kaya, mai taimaka wa Gwamna na Musamman na II kan Harkokin Al’umma
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali, rashin da’a ko cin zarafin mukami ba, kuma duk wani abu da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya ko rage amincewar jama’a ga gwamnati ba za a lamunce shi ba.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Gombe kudirin gwamnatinsa na bin doka da oda, gaskiya da riƙon amana, tare da ɗaukar tsauraran matakai domin kare zaman lafiya da ci-gaban da jihar ta samu.
