News
Wasu Yan Bindiga Sun Sace Kansila Da Wasu Mutum 2 A Jahar Kaduna

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Kansilan gundumar Garu da ke Karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, Alhaji Sabitu Ahmad, da wasu mutum biyu.
Rahotanni na nuni da cewa ’yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a yankin Anguwar Mai Taro da ke a Karamar Hukumar, inda Kansilan ke zaune suka dauke shi da wata mata a unguwar a ranar 19 ga watan Agustan da muke ciki.
Ana Ci Gaba Da Gwabza Ƙazamin Fada Tsakanin ISWAP da Boko Haram
Kazalika, an sace wani mutum daya a unguwar Dankande a ranar 18 ga watan Agusta, duk a Karamar Hukumar ta Soba.
Lawal Sani, wani matashi a yankin ya bayyana wa Aminiya cewa Kansilan da aka sace kuma shi ne kakakin Kansaloli na Karamar Hukumar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, bai amsa wayarsa ba da kuma sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya aike masa.
Shi kuwa mai magana da yawun Gwamnar Jihar, Mohammmed Lawan Shehu da aka tuntube shi cewa ya yi har yanzu ba a sanar da shi a hukumance ba.