News
An tsinci gawar wata yarinya ‘yar shekara 16 da ta bata a cikin rijiya a Jigawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
An jefar da gawar wata yarinya ‘yar shekara 16 a cikin rijiya a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Wani dan uwan mamacin ne ya shaidawa Jaridar DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a kauyen Beguwa a ranar Asabar din da ta gabata.
Wasu Yan Bindiga Sun Sace Kansila Da Wasu Mutum 2 A Jahar Kaduna
Ya ce an fara bayyana cewa marigayiyar ta bace kafin a gano gawarta a ranar Laraba, kwanaki hudu da faruwar lamarin, yayin da wasu manoma da ke kan hanyarsu ta zuwa gona suka ji wani wari.
Ya yi zargin cewa saurayin nata da abokansa ne suka yi wa marigayiyar fyade,inda suka jefar da gawarta a cikin wata rijiya da ke wajen kauyen.
Don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da kungiyoyin farar hula da su sanya ido a kan lamarin tare da tabbatar da an yi adalci.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP. Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce ‘yan sanda sun samu rahoton cewa an gano gawar yarinyar a wata rijiya da ke wajen kauyen Beguwa a Ringim.
Ya ce binciken ya kai ga cafke babban wanda ake zargin, wanda tun da farko an gan ta tare da marigayiyar a wajen wani daurin aure kafin a ce ta bace.
Shiisu ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma zai bayar da cikakken bayani kan lamarin.