Connect with us

News

Kotu Ta Ƙwace Wani Wurin Haƙar Ma’adanai  Na ‘Yan China

Published

on

Illegal mining site

Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas ta bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori da aka samu daga hannun wasu ‘yan ƙasar China da ake zargi da gudanar da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar Ogun, tare da mayar da shi mallakin Gwamnatin Tarayya.

Mai shari’a Daniel Osiagor ne ya yanke hukuncin bayan wata bukata da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) reshen Ikoyi ta gabatar ta hannun lauyarta, Bilkisu Buhari.

Advertisement

Kwantena Ta Murkushe Wata Motar Haya

Kadarorin da aka kwace sun haɗa da wani wurin haƙar ma’adanai da ke bayan fadar Baale a titin Ileposo da ke Ode-Remo a jihar Ogun,

Advertisement

Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da motar Toyota 4Runner, manyan motoci uku ɗauke da ma’adanai masu yawa, da kuma wani kwantena mai ɗauke da buhuna 3,210 na ma’adanan mica da lithium.

EFCC ta shaida wa kotun cewa ta nemi a ba ta ikon kula da kadarorin tare da sayar da su bisa sashe na 330 na dokar gudanar da shari’ar manyan laifuka ta shekarar 2015 da sauran dokoki masu alaƙa.

Advertisement

Hukumar ta kuma roƙi kotun da ta ba ta damar haɗa kai da Hukumar Binciken Albarkatun Ƙasa ta Najeriya wajen sayar da kadarorin tare da ajiye kuɗaɗen da za a samu a asusun banki mai ruwa har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar da ake yi wa waɗanda ake zargi.

Rahoton ya ce ana tattara ma’adanan daga wurare daban-daban na ƙasar nan zuwa yankin Ode-Remo, inda ake tace su tare da shirya jigilar su ta tashar jiragen ruwa ta Apapa da kuma filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas.

Advertisement

Hukumar ta ce ta gudanar da samame da sanyin safiyar ranar 9 ga Mayun 2025, inda ta kama wasu ‘yan ƙasar China biyu da ake zargin su ne jagororin harkar, tare da wasu ‘yan Najeriya shida a wurin haƙar ma’adanan.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Channelstv

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending