News
Kotu Ta Kori Shari’ar Neman Hana Jonathan Takara
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.
Wani tsagi na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ne a makon da ya gabata ya bai wa Jonathan takardar amincewa domin ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa shi kaɗai a jam’iyyar.
Kotu Ta Ƙwace Wani Wurin Haƙar Ma’adanai Na ‘Yan China
Sai dai wani mutum mai suna Johnmary Jideobi ya shigar da ƙara yana neman kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Mai ƙarar ya kuma roƙi kotun ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Independent National Electoral Commission, karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Ya buƙaci kotun ta fayyace ko sashe na 137(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya haramta wa Jonathan sake neman kujerar shugaban ƙasa.
Sai dai a hukuncin da ya yanke ranar Talata, Mai shari’a Peter Lifu ya bayyana cewa Jonathan na da cikakkiyar damar shiga takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
