Connect with us

News

Kotu Ta Haramtawa Jami’an  FRSC (Road Safety) Tare Motoci A Titunan Kano

Published

on

FRSC e1784227557188 (1)

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa FRSC ba ta da hurumin gudanar da ayyukanta a kan hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi.

Kotun ta kuma bayyana cewa matakan da jami’an FRSC su ke ɗauka a cikin birnin Kano ba ya bisa ƙa’ida, kuma su na take haƙƙin al’umma.

Yayin da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis kan ƙarar da lauya Abba Hikima, ya shigar a kan FRSC, mai shari’a M. S. Shuaibu ya ce jami’an hukumar sun wuce iyakokin ikon da doka ta ba su lokacin da su ka tare, su ka tsayar, su ka yi wa direbobi tambayoyi tare da ɓata musu lokaci a hanyoyin cikin gari.

Kotu Ta Umarci A Ƙwace Kadarorin Naira Biliyan 212.8 Da Aka Alaƙanta Da Tsohon AGF, Abubakar Malami

Kotun ta bayyana cewa irin wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, musamman sashe na 35 da na 41, waɗanda su ka tanadi haƙƙin ƴancin kai da kuma yancin zirga-zirga.

Kotun ta amince da duk manyan buƙatun da mai karar ya gabatar, ciki har da bayar da umarnin haramta wa jami’an FRSC ci gaba da tsayar da direbobi ko muzgunawa masu amfani da hanyoyin jihar Kano ba tare da cikakken ikon doka ba.

Advertisement

Haka kuma kotun ta umurci FRSC da ta wallafa nemi afuwa ga jama’a a wata jaridar ƙasa, tare da biyan mai ƙarar diyyar Naira 800,000 a matsayin diyya da kuɗin shari’a.

Lamarin ya samo asali ne a watan Yulin shekarar da ta gabata, lokacin da jami’an FRSC su ka kafa shingayen bincike a hanyoyin cikin birnin Kano, inda su ka riƙa tsayar da direbobi, ciki har da Abba Hikima, su na neman lasisin tuƙi tare da yi musu tambayoyi ba tare da sun aikata wani laifin karya dokar hanya ba.

Daga nan ne Hikima ya garzaya babbar kotun tarayya domin ƙalubalantar abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa.

A cewarsa, ikon da dokar FRSC ta tanada ya taƙaita ne ga manyan hanyoyin gwamnatin tarayya kawai, ba ya shafar hanyoyin jihohi ko na ƙananan hukumomi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending