Connect with us

News

Yadda Direbobi masu ganganci suka yi Ajalin Ma’aikatan FRSC Biyar

Published

on

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa wasu direbobi masu tukin ganganci sun kashe ma’aikatan hukumar guda biyar a cikin watan Satumba 2025, yayin da suke kan aikin su a wurare daban-daban na kasar.

A cewar Olusegun Ogungbemide, jami’in hulda da jama’a na FRSC, mutuwar ta faru ne a sassa biyar na kasar: ranar 6 ga Satumba a Ekiti, ranar 8 a Ogun, ranar 15 a Taraba, ranar 19 a Jos (Filato), da ranar 24 a Obollo.

Kungiyar One Kano Agenda Ta Yi Allah Wadai Da Janye Jami’an Tsaro Daga Bikin Cikar Najeriya Shekaru 65 A Kano

Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya bayyana lamarin a matsayin “abin bakin ciki matuka” sannan ya umurci a gurfanar da duk direbobin da ke da hannu a kotu.

Hukumar ta nuna damuwa kan yadda kariya ga ma’aikatan ta ke tabarbarewa, inda ta ce, “Sakamakon gudun ababen hawa, jami’anmu na kara fuskantar hare-hare, garkuwa da mutane da sauran barazana.”

Shehu Mohammed ya gargadi cewa rundunar ba za ta lamuntar ayyukan da ke barazana ga ma’aikatanta ba, yana mai jaddada cewa masu laifi za su fuskanci hukunci mai tsanani a gaban shari’a.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending