Connect with us

News

Kungiyar One Kano Agenda Ta Yi Allah Wadai Da Janye Jami’an Tsaro Daga Bikin Cikar Najeriya Shekaru 65 A Kano

Published

on

IMG 20251002 WA0015
Taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Sakatariyar ‘Yan Jaridu ta Jihar Kano

Kungiyar One Kano Agenda, wadda ke fafutukar zaman lafiya da ci gaban Jihar Kano, ta bayyana damuwarta kan matakin da aka dauka na janye jami’an tsaro daga wajen bikin cikar Najeriya shekaru 65 a Kano, matakin da ta ce bai da wani dalili mai karfi.

Fistula Foundation Ta Yi Wa Mata Aiki Kyauta, Ta Raba Musu Kayan Dogaro Da Kai A Kano

A taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Sakatariyar ‘Yan Jaridu ta Jihar Kano, Abbas Abdullahi, mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana cewa:

Advertisement

“Abin da ya faru a bikin, musamman janye jami’an tsaro daga wajen taron ranar ‘yancin kai ba tare da wani dalili mai karfi ba a mintuna 30 kafin fara taron, ya nuna an yi shi ne da nufin siyasa, domin kawo rudani da rashin kwanciyar hankali a jihar.”

Kungiyar ta ce yayin da sauran jihohi ke gudanar da bukukuwansu tare da cikakken hadin gwiwar ‘yan sanda, Kano ta fuskanci umarni na musamman daga Abuja, wanda ya nuna an ware jihar daga tsarin tsaro na kasa.

Advertisement

“Wannan ba sabon abu bane. Mun riga mun ga yadda wasu ke yiwa al’adun gargajiya na Kano barna domin tada rikici da kawo rashin jituwa. Burinsu bayyananne ne — su ci moriyar siyasa ne kawai, ba tare da la’akari da zaman lafiya da ci gaban al’umma ba,” in ji kungiyar.

Kungiyar ta yi kira ga matasa masu kishin zaman lafiya su kasance masu lura, tare da jan hankali kada su bari a yi amfani da su wajen siyasar da ke kawo rudani. Ta kara da cewa:

Advertisement

“Kano gida ne na kowa, kuma ya kamata kowa ya tsaya tsayin daka wajen kare zaman lafiya.”

Abbas Abdullahi ya kuma goyi bayan bukatar Gwamna Abba Kabir Yusuf na neman Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya canja kwamishinan ‘yan sanda na Kano nan take domin rage tashin hankali, da nuna sahihiyar muradin gwamnatin tarayya na tabbatar da zaman lafiya da mutunta dokokin kasa.

Advertisement

Kungiyar ta yaba wa jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tabbatar da cewa bikin ya gudana yadda ya kamata duk da katsalandan da aka yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending