Connect with us

News

Fistula Foundation Ta Yi Wa Mata Aiki Kyauta, Ta Raba Musu Kayan Dogaro Da Kai A Kano

Published

on

IMG 20251002 WA0008

Gidauniyar Fistula Foundation Nigeria, wadda ke tallafawa mata masu fama da lalurar yoyon fitsari, ta gudanar da taron yaye wasu mata da aka yi wa aikin gyara kyauta, tare da raba musu kayan sana’o’i domin su dogara da kansu.

Taron, wanda aka shirya a harabar cibiyar kula da masu fama da wannan lalura dake Unguwar Kwalli, Kano, ya samu halartar jami’an gwamnati, wakilai daga ƙasashen waje, da ƙungiyoyi masu zaman kansu. Haka kuma, ɗaya daga cikin shugabannin gidauniyar daga Amurka ta halarci taron.

Advertisement

NAPTIP ta cafke mutane biyar da ake zargi da safarar mutane, ta kuɓutar da mutum 24 a Abuja

Shugaban gidauniyar, Musa Isah, wanda aka fi sani da Baba Musa, ya bayyana cewa manufa ta shirya wannan biki ita ce nuna farin cikin nasarar da suka samu wajen taimaka wa mata da ke fama da yoyon fitsari ta hanyar yi musu aiki kyauta da kuma samar musu da kayan dogaro da kai.

“Makasudin wannan shiri shi ne mu ga waɗannan mata sun dawo cikin koshin lafiya, kuma sun samu damar dogaro da kansu ta hanyar sana’a. Wannan lalura tana lalata rayuwar mata da dama, amma muna ƙoƙarin dawo da martabarsu,” in ji Baba Musa.

Advertisement

Baba Musa ya ƙara da cewa gidauniyar ta samu nasara wajen inganta cibiyar kula da masu yoyon fitsari da ke Kwalli, wanda hakan ya sauƙaƙa aikin kula da lafiyar mata masu fama da wannan matsala.

“Mun gyara cibiyar tare da samar da kayan aiki na zamani da ƙwararrun ma’aikata, domin tabbatar da cewa mata da yawa sun samu kulawa mai inganci,” in ji shi.

Advertisement

Wakilin Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano, Malam Muhammad Sabo Iliyasu, ya yaba da ƙoƙarin gidauniyar bisa gudunmawar da take bayarwa wajen dawo da martabar mata masu fama da yoyon fitsari.

“Wannan aiki abin yabawa ne sosai. Gidauniyar tana taimaka wa mata da suka yi fama da wannan matsala tsawon shekaru, sannan tana ba su kayan sana’a domin su fara sabuwar rayuwa cikin ƙima da mutunci,” in ji Sabo.

Advertisement

Taron ya gudana cikin farin ciki da nuna godiya daga waɗanda suka amfana, inda da dama daga cikinsu suka bayyana cewa tallafin ya ba su damar sake tsayawa da kafafunsu bayan dogon lokaci na wahala da ƙunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending