News
NAPTIP ta cafke mutane biyar da ake zargi da safarar mutane, ta kuɓutar da mutum 24 a Abuja
Hukumar yaƙi da safarar mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutane biyar da ake zargi da hannu a safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Vincent Adekoye, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce cikin waɗanda aka kama har da wani mutum da ake zargin ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.
Gwamna Fubara Ya Kori Dukkan Kwamishinoni Da Manyan Jami’an Gwamnatin Jihar
Adekoye ya ce samamen, wanda aka gudanar bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin Babbar Daraktar NAPTIP, Binta Adamu Bello.
Ya ce cikin waɗanda aka kama akwai wani babban jami’in tsaro da ke cikin ƙungiyar masu safarar mutane a yankin kudu maso yamma na ƙasar.
“Mun kuɓutar da yara da matasa masu shekaru tsakanin 15 da 26, waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi, Sudan, Masar, Saudiyya, Bahrain da Afghanistan,” in ji Adekoye.
A cewarsa, ɗaya daga cikin waɗanda aka kuɓutar ta sha alwashin ganin cewa an gurfanar da mahaifinta a kotu bisa yunƙurin safararta da ya yi zuwa Iraƙi.
Haka kuma wata daga cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta bayyana cewa mahaifiyarta ce ta tilasta mata ta amince da tafiya zuwa Turai don yin aikin da za ta rika samun daloli.
NAPTIP ta ce za ta ci gaba da kai sama-samar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da safarar mutane da kuma tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu a cikin irin waɗannan laifuka sun fuskanci hukunci.
