News
NAPTIP Ta Ceto Wasu Yara Takwas Da Aka Sace Daga Kano A Gidan Marayu A Delta
Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara takwas da ake zargin an sace su daga jihohin arewacin ƙasar ciki har da Kano, aka kuma kai su wani gidan marayu a Asaba, babban birnin jihar Delta.
Kakakin hukumar, Vincent Adekoye, ya bayyana cewa aikin ya samu ne da hadin gwiwar jami’an tsaro, ciki har da Hukumar DSS, ’yan sanda da jami’an Civil Defence.
SHEKARAR 2027 : Karfin Sanata Barau Ya Dogara Kan Kulawarsa Da Cigaban Dan Adam
Rahoton hukumar ya ce shekaru da dama kenan iyaye daga Kano da wasu jihohin makwabta ke ta kai ƙorafi kan ɓacewar ’ya’yansu, inda ake zargin wasu ƙungiyoyi na amfani da sunan ’yan kasuwa wajen yaudarar yara ’yan shekaru biyu zuwa goma, daga baya su tafi da su ba tare da izini ba.
A samamen da aka kai gidan marayun, an gano yara sama da 70 ciki har da jarirai, sai dai daga cikinsu yara takwas aka tabbatar daga Kano su ke, kuma an gano su ta hanyar hotuna da siffofin da iyayensu suka bayyana.
Shugabar NAPTIP, Binta Bello, ta bayyana damuwa kan yadda wasu gidajen marayu da cibiyoyin kula da yara ke zama mafaka ga ayyukan safarar mutane
